Mutane dadama suna da wasu tambayoyi da suke musu kaikayi kuma suke neman amsa ruwa a jallo akan Tarihin Janar Muhammadu Buhari Shugaban Kasar Nigeria wanda yake mulki yanzu, idan kana bibiyar mu yau zamu Fede Biri Har Wutsiya game da tarihin buhari.
Wannan rubutu zai wanke duk wani kokwanto da kuma bada amsa ga mai neman sanin waye ainihin Muhammadu Buhari, muna fatan zaku karanta wannan rubutu cikin nutsuwa kuma har karshe.
Waye Muhammadu Buhari?
Buhari Adamu wanda akafi sani da Muhammadu Buhari an haife shi a ranar 17 ga watan Disamba 1941 a garin birnin Daura na jahar Katsina State,
Yayi makarantar Primary da kuma Secondary duk a Daura wanda daga bisani yashiga makarantar horas da sojoji dake Kaduna a shekarar 1962.
Ya kuma yi makarantar koyon yaki dake America har aka bashi mukamin 2ND Lieutenet a shekarar 1963, buhari yataba rike mukamin gwamnan mulkin soja na jihar Borno daga shekarar 1975 zuwa 1976.
Tarihin Mulkin Buhari Na Soja
Sojoji sun yiwa buhari juyin mulki a 1985 kuma suka saka shi a kurkuku tsawon shekara uku, sai ranar 13 ga watan Disamba a shekarar 1988 sojoji suka saki Buhari daga nan ne kuma yafara shawarar shiga Siyasa.
Mulkin Buhari na soja bai dade sosai ba domin kuwa ko shekara daya bai cika ba, sannan yasha wahala sosai a hanun wanda suka kwace mulki daga wajen sa.
Shekarun Buhari Nawa?
Idan mukayi lissafi da cewa an haifi shi a17 ga watan Disamba na 1941 zuwa 2021 zai kama shekarun Muhammadu Bahuri 80 a duniya (Shekarun Buhari Tamanin) da wasu watanni.
Wannan lissafi dai mun samo shie ne daga shafin Wikipedia wanda kuma shine gaskiya, don haka duk wasu labarai daza kagani akan shekarun buhari sabanin wannan zamu iya cewa ba gaskiya bane.
Karanta Wannan: Babu Wanda Yayi Aikin Danayi Daga 1999 zuwa 2021 - Buhari
Waye Mahaifin Buhari?
Sunan mahaifin Buhari Adamu Buhari (Bafallaje) sai dai babu wani cikakken bayani akan mahifin buhari kawai dai mun san cewa bafulatani ne, bayan wannan babu wani karin haske akansa.
Tarihin mahaifin buhari wato Adamu babu shi a manyan jaridu, wannan dalili yasa babu wasu bayanai daza mu iya kawowa wanda ya wuce wannan.
Menene Yaren Buhari?
Buhari dai ainihin bafulatani ne wanda aka haifa a Daura ta jahar Katsina, don haka za a iya cewa cikin kalma daya Janar Muhammadu Bahari cikakken dan Fulani ne.
Yaushe Buhari Yayi Auren Fari?
Muhammadu Buhari yayi aurensa na farko a shekarar 1971 da matarsa Safinatu Yusuf (ta rasu a 2006) inda suka haifi 'ya 'ya biyar kafin rasuwarta, lokacin da buhari ya auri safinatu yana da shekara 30 a duniya.
'Ya 'Yan Safinatu Matar Buhari Tafarko
- Zulaihat Buhari (ta rasu)
- Fatima Buhari
- Musa Buhari (ya rasu)
- Hadiza Buhari
- Safinatu Buhari
Buhari da Safinatu sunyi zama tsawon shekaru 30 da wani abu kafin Allah yakarbi rayuwarta a shekarar 2006 daga nan yazama gwauro kafin ya auri Aisha.
Auren Muhammadu Buhari Da Aisha Halliru Buhari
Muhammadu ya Auri Aisha Halliru Buhari wato matarsa ta yanzu a shekarar 1989 zuwa har wannan lokaci da muke ciki wato 2021, sun haifi 'ya 'ya 5 wanda Allah yayiwa tsawon kwana gaba daya, ga jerin yaran da Aisha ta haifa:
'Ya 'Yan Aisha Halliru Matar Buhari ta Yanzu
- Halima Buhari
- Zahra Buhari,
- Yusuf Muhammadu Buhari
- Aisha Hanan Buhari
- Amina Buhari
Wadannan sune jerin matan Buhari da kuma tarihin yadda ya aure su, idan kayi lissafi Allah ya albarkace shi da samun 'ya 'ya 10 har da wanda suka mutu guda 2 wanda yanzu haka yana da guda 8 da suke rayuwa a wannan duniya.
Karanta Wannan: Yusuf Buhari Net Worth 2020 - 2021, Phone Number, Wedding, Accident, Biography, Age
Tarihin Siyasar Muhammadu Buhari
Buhari ya shiga harkar Siyasa a shakarar 2003 wanda yafara tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyyar ANPP wanda bai samu nasara ba, ya sake fitowa takarar shugabancin Nigeria a shekarar 2007 duk dai a jam'iyyar ANPP nan ma daga karshe yafadi.
Rashin nasarar Buhari a siyasa bai sa gwaiwarsa ta karye ba domin ya sake fitowa takara a 2011 a jam'iyyar CPC wanda ya kikire ta, sai dai kuma wannan shekarar ma bai yi nasara ba inda yasha kaye a hanun Goodluck Jonathan.
Jam'iyyun Siyasar Buhari
- ANNP
- CPC
- APC
Mai nema baya gajiya kuma wata rana zai samu, domin kuwa takarar buhari tayi nasara a shekarar 2015 inda aka zabe shi a tsohuwar jam'iyyarsa wanda ya chanzawa suna daga CPC zuwa APC a matsayin shugaban Nigeria kuma da gagarimin rinjaye.
Bayan shafe tsawon shekaru hudu a matsayin shugaba buhari yasake cin zabe a 2019 inda yasake zarcewa karo na 2 wanda har zuwa yanzu shine yake mulikin kasar Nigeria.
Rayuwar Buhari A Yau
A yanzu haka Muhammadu Buhari yana kan mulkin kasar Nigeria inda yake cikin shekara ta 6 da shugabanci, zuwa shekarar 2023 buhari zai sauka daga kujerar mulkin Najeriya kuma lokin zai kasance shekarunsa 82 a duniya.
Babban makasudin zaben shugaba buhari dai a 2015 shine saboda rashin tsaro daya addabi kasar nan dalilin kungiyoyin ta'addanci musamman a yankin arewancin najeriya.
Za a iya cewa Janar Muhammadu Buhari yana cikin manyan mutane da kasar Nigeria take alfahari dasu, sannan ya kafa babban tarihi a ciki da wajen kasar nan daga nan har bayan mutuwarsa.
Kuci Gaba Da Ziyatar www.izzarso.com.ng
Post a Comment