Tarihin KB International Jarumin Kannywood

Tarihin KB International
Tarihin KB International

Tarihin KB International jarumin kannywood, yanzu dai ana samun jarumai a masana'antar shirya fina finan Hausa wanda suke yin suna ta wajen fitowa a wakokin hausa. KB International yana daya daga cikin wadannan jarumai kuma yau zamu kawo muku tarihin rayuwar kb international.

Tarihin KB International Biography (Farko)

Wannan jarumi dai kusan za a iya cewa bai jima da shigowa kannywood ba, domin kuwa bazai wuce shekara biyu zuwa uku ba amma yayi suna sosai sanadin fitowa a wakokin hausa na video. saboda haka yasa mafi yawan masoyansa da dama sun san shine wajen mamin din waka.

Lokacin da KB International yazo masana'antar shirya fina finan hausa lokaci ne da ake yayin saka wakokin hausa a Youtube musamman na wakokin soyayya, don haka a wannan lokaci yasamu nasarar haduwa da manyan masu shirya Hausa Videos Songs kamar irin su Sunusi Oscar 442, Aminu S Bono, Saifullahi Safzor da sauransu.

Ya fito a wakokin hausa dayawa sannan an hada shi da jaruman kannywood mata wanda ake yayi a lokacin irin su Aisha Najamu Izzar So, Momee Gombe, Rakiya Musa, da sauransu, sannan ya hau wakokin manyan mawakan hausa irin su Hamisu Breaker, Garzali Miko, Haleefa SK, Isah Ayagi, Auta MG Boy, Umar M Shariff da kuma Sani Ahmad.


KB International Songs
KB International Songs

KB International Songs

KB International ya hau wakokin hausa da dama wanda baza su kirgu ba, sai dai yafi hawa wakokin Hamisu Breaker wanda shima yanzu tauraruwarsa take haskawa. ga wasu daga jerin wakokin da KB ya samu fitowa wanda kuma wadannan wakokin sunyi suna sosai.

KB International Songs:
  1. Kalaman Soyayya
  2. Rakiyar So
  3. Haduwar Jini
  4. Zumar Kauna
  5. Mai Yayemin Damuwa
  6. Laila
  7. So Kamar Gizo
  8. Zinariya
  9. Zance Da Zuciya
  10. Tauraruwar Zuciya

Wadannan wasu kenan daga wakokin da jarumin kannywood KB International ya fito tare da manyan jarumai mata, idan za a duba yawancin wakokinsa na video da jaruma Momee Gombe yayi su sai kuma Rakiya Musa 'yar kasar Niger.

Tarihin KB International (Karshe) 

Wannan dai shine takaicaccen tarihin jarumin kannywood kb (KB International Biography) wanda mukayi binceke kafin mu rubuta, sai dai zaku ga bamu kawo sunan iyayensa da kuma asalin garin da aka haifeshi ba. hakan yafaru ne saboda bamu samu wani cikakken bayani akan rayuwar KB International ba.

Idan muka samu wadannan bayanai zamu saka su acikin wannan shafi, don haka sai ku kasance damu domin samun rahotanni daga masana'antar shirya fina finan Hausa wato Kannywood.

Kuci Gaba Da Ziyatar www.izzarso.com.ng

Post a Comment

Previous Post Next Post