Rahama Sadau Zata Fito a Khuda Haafiz Chapter 2 Shirin Film Din Bollywood

Rahama Sadau Khuda Haafiz Chapter 2
Rahama Sadau Khuda Haafiz Chapter 2

Rahama Sadau Zata Fito a Khuda Haafiz Chapter 2 Shirin Film Din Bollywood

Daga karshe dai burin shahararriyar jarumar Kannywood Rahama Sadau yacika anfara shirin film da ita a Bollywood, wanda yanzu haka ana cikin daukar wannan film a kasar India.

Dama jarumar tajima tana mafarkin fitowa a fina finan kasar India, sai dai mutane dadama suna ganin cewa kamar burin nata bazai samu cika ba saboda zai wahala masu shirya film a Bollywood su yadda su sakata a fina finan su.


Amma masu karin magana suna cewa 'Duk Mai Nema Wata Rana Zai Samu' haka kuwa ta kasance, Rahama Sadau tayi nasarar cimma burinta na bayyana a film din indiyawa wanda yanzu haka har anfara daukar wani sabon shiri da ita mai suna Khuda Haafiz Chapter 2.


Rahama Sadau Khuda Haafiz Chapter 2

Khuda Haafiz Chapter 2 Wanda Rahama Sadau Zata Fito Aciki


Wannan shiri dai wani sanannen film ne wanda aka fidda na dayansa a 2020 (Khuda Haafiz Chapter 1), film din yasamu kasuwa sosai wanda hakan yasa yanzu ake shirya na 2 tare da jarumar Kannywood.


Har yanzu dai babu wanda yasan ya akayi Rahama Sadau tasamu shiga cikin wannan babban film, wanda har anga hotunan jarumar tare shahararren jarumin India mai suna Vidyut Jammwal wanda shine babban jarumi a film din kuma hakan yake sake tabbatar da cewa lallai za aga Rahama a Khuda Haafiz Chapter 2.


An Kori Rahama Sadau Daga Kannywood Saboda Shigar Banza


Kafin dai jarumar tasamu zuwa India wasu abubuwa sun faru da ita a tsohuwar masana'antar da take fitowa a fina finai wato Kannywood, wannan abu daya faru sai da yajawo aka kori jarumar daga shirin film kwata-kwata.


Abin daya jawo wannan hatsaniya dai shine Rahama Sadau takarbi tallan wani kayan sawa na mata wanda suka nuna bayanta tsirara, wannan kaya sunyi baram-baram da dokar Muslunci da kuma al'adar hausawa wanda hakan yajawo akai ta tsinewa jarumar daga karshe ma aka koreta daga masana'antar shirya fina finan Hausa wato Kannywood.


Rahama Sadau Khuda Haafiz Chapter 2

A Wane Matsayi Rahama Sadau Zata Fito a Khuda Haafiz Chapter 2?


Babu wanda yasan takamaiman wane mataki za a fito da Rahama a wannan sabon shiri na India, sai dai masu hasashe suna ganin zai wahala daga zuwanta su bata damar fitowa a babbar jaruma batare da sunga irin rawar daza ta takaba.


Watakila Rahama Sadau tasamu fitowa a mataimakiyar jaruma a wannan shiri ko kuma kasa da haka, koma dai yaya tasamu, wannan itace damarta wanda nan gaba za a iya sanyata a babbar jaruma a manyan fina finan Bollywood.


Manyan jaruman Kannywood dai sun taya Rahama Sadau farin cikin samun shiga babbar masana'antar shirya fina finai ta Bollywood, wadannan jarumai sune kamar Ali Nuhu, Sadik Sani Sadik, Ado Gwanja, da dai sauransu.


Rahama Sadau Khuda Haafiz Chapter 2

Shin Rahama Sadau Ci Gaba Tasamu Kokuma Koma Baya?


Idan aka duba tsarin shirya film na duniya da kuma ribar da ake samu to gaskiya Rahama ba karamin ci gaba tasamu a sana'arta ba, domin kuwa Bollywood suna samun makudan kudade a fina finan su wanda ake kalla a duk fadin duniya.


Sabanin fina finan Hausa wanda iya kasar nan ne suke kalla suma akwai yankin da basu damu da film din Hausa ba, amma akwai kasashen ketare makwabta kamar Niger, Chadi, Kamaru suna kallon film din Hausa.


Rahama Sadau tasamu ci gaba sosai idan aka duba haka, sai dai wasu suna ganin wajen abin daya shafi Addini da kuma al'ada a wannan wajen koma baya tasamu.


Domin tsarin da Bollywood suke bi wajen shirya film yasaba da dokar Muslunci da kuma al'adar Hausawa, domin suna aikata abubuwa wanda anan bai dace ana nuna su ga Al'ummah ba.


Rahama Sadau Zata Fito a Khuda Haafiz Chapter 2 Shirin Film Din Bollywood India


Yanzu burin jarumar na 1 yafara cika saura burinta na 2 shine fitowa a film daya tare da jarumar Bollywood Priyanka Chopra wanda Rahama Sadau tajima tana mafarki.


Wannan shine karshe wannan sharhi namu akan fitawar jarumar Kannywood a cikin shirin film din Bollywood Khuda Haafiz Chapter 2, muna fatan wannan rubutu ya kayatar daku.


Kuci Gaba Da Ziyartar www.izzarso.com.ng


Post a Comment

Previous Post Next Post