Maryam Malika Tace Mutane Suna Mata Kallon Mace Mai Masifa Saboda Idanuwanta

maryam malika


Maryam Malika Tace Mutane Suna Mata Kallon Mace Mai Masifa Saboda Idanuwanta


Kamar yadda BBC Hausa tasaba kawo tattanawa da manyan jaruman Kannywood duk ranar Alhamis a cikin shirin su mai suna 'Daga Bakin Mai Ita'


Wannan karon sunyi hira da tsohuwar jarumar Kannywood wanda yanzu tadawo masana'antar domin ci gaba da fitowa a fina finai wato Maryam Malika.


A cikin hirar tata da BBC Hausa ta bayyana abubuwa dadama wanda suka shafi rayuwar ta da kuma sana'arta wato Hausa Film.


Maryam Malika


Tarihin Maryam Malika Daga Bakinta


Sunan Maryam Malika dai na asali shine Maryam Muhammad kuma haifaffiyar garin Kaduna State ce, Maryam tayi makarantar Firamire da kuma Sakandire duk a Kaduna.


Jarumar tashiga kungiyar Kannywood a shekarar 2010 kuma anfara sakata a Wasila Hausa film, tace tayi sha'awar fitowa a fina finan Hausa saboda yadda taga suna fadakarwa itama tace bari tazo tabada tata gudummawar.


Maryam Malika tace jarumi Ali Nuhu shine yayi mata hanyar shiga Kannywood kuma tayi fina finai wanda take ji dasu kamar Malika, Adon Gari, Kona Gari, Soyayyar Facebook, dadai sauransu.


BBC Hausa ta tambayeta su wanene kawayenta a cikin jaruman Kannywood, ta bada amsa da cewa kawayenta sune Fati S,U da kuma Bilkisu Shema.


Maryam tace bata da Saurayi a Kannywood sannan saurayin data farayi a Duniya shine mijin data aure kuma yanzu basa tare dashi.


Maryam Malika


Maryam Malika ta amsa tambayar cewa 'Wasu Suna Cewa Matan Kannywood Basa Zaman Aure' tace ba haka bane, kawai mutane suna fadar abin daba su tabbatar da shi ba kuma basu da shaida akansa.


Tace kuma 'Mutane Suna Min Kallon Masifaffiya' Maryam tace wasu suna cewa Idanuwanta a tsai tsaye suke shiyasa suke kallon zatayi masifa bayan kuma ba haka bane,


Maryam Malika ta bayyana abinda yake sata bakin ciki duk lokacin data tuna dashi wato mutuwar yar uwarta Jaruma Balaraba Muhammad, Balaraba dai yayarta ne wanda ta rasu a ranar Aurenta da jarumin Kannywood Shu'aibu Lawan Kumarci.


A karshe tace babban burinta shine tasamu damar daza ta taimakawa Gajiyayyu da Marayu, sannan ta bayyana cewa ko yau tasamu miji na gari zata koma gidan Aure.


Kuci Gaba Da Ziyartar www.izzarso.com.ng



Post a Comment

Previous Post Next Post